Sanata mai wakiltar Yankin Adamawa ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Aminu Iya Abbas, ya shirya horo na tsawon kwana biyar kan fasahar gyaran wutar lantarki ta hasken rana ga matasa 50 domin su zama masu horarwa ga wasu matasa 500 a fadin yankin.
Wannan taron wanda ya fara makon da ya gabata a dakin taro na NUT dake birnin Yola, an shirya shi ne tare da haɗin gwiwar Hukumar Makamashi ta Najeriya da kuma Shining Structure Synergy Limited.
Da yake magana a lokacin horon, Sanata Aminu Iya Abbas wanda aka wakilta ta hannun ɗaya daga cikin abokan aikinsa, wanda kuma shine Mai Baiwa Gwamnan Adamawa Shawara Kan Gudanar da Mulki, Dr. Adamu Mallam Babikkoi, ya ce an shirya wannan horon ne domin bai wa matasa a yankin horo kan fasahar sabunta makamashi domin su tafi dai da zamani.
Ya bayyana cewa an zaɓi waɗanda suka ci gajiyar horon daga ƙananan hukumomi 7 da suka haɗa da Hong, Gombi, Song, Girei, Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da kuma karamar Hukumar Fufore da suke kunshi yankin Adamawa ta Tsakiya.
Sanata Iya Abbas ya ƙara da cewa za a ba waɗanda suka ci gajiyar horon kayan aiki bayan kammala horon, wanda zai taimaka musu wajen horar da wasu da kuma zama jagora a gyare-gyaren da kuma shigar da tsarin hasken rana.
A nasa jawabin, Daraktan Hukumar Makamashi ta Najeriya, wanda Alhaji Na’yaya Garba ya wakilta, ya bayyana cewa an bai wa mahalarta horon ƙwarewar da ake buƙata wajen samun fasahar sabunta makamashi ta hanyar tsarin haɗin gwiwar hasken rana. Ya kuma shawarci mahalarta su yi amfani da ilimin da suka samu domin amfanin al’umma.
Shi ma, Mista Nafi’u Tijjani, wanda ya jagoranci horon a Yola tare da Na’yaya Garba a madadin Hukumar Makamashi, ya yaba wa Sanata Aminu Iya Abbas kan jajircewarsa wajen bai wa matasa a mazaɓarsa dabaru daban-daban domin su dogara da kansu.
Malam Aminu Alkali, wanda shi ne ɗaya daga cikin masu ba da horon, ya tunatar da mahalarta horon su gudanar da cikakken bincike kafin shigar da na’urorin.
A nasu bangareny, Mataimakiyar Shugaban Ƙaramar Hukumar Girei Hon. Luri Zephaniah hada da Dr. Job Gundiri, yayin da suke kira ga waɗanda suka ci gajiyar horon su yi amfani da ƙwarewar da suka samu da kayan aikin da za a ba su domin ci gaban Adamawa ta Tsakiya da jihar baki ɗaya, sun bayyana horon a matsayin abin da ya zo a kan gaba.
A madadin sauran waɗanda suka ci gajiyar horon, Imamu Garba da Hingino Enock sun nuna godiyarsu ga Sanata Aminu Iya Abbas saboda wannan horon, suna cewa horon ya ba su ƙwarewar da ta dace wajen shigar da gyaran wutar lantarki ta hasken rana.