By Abubakar Muhammad Adamu
Majalisar Dokokin Jihar Adamawa ta amince da kudirin doka da ke soke Dokar Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Musulmi ta Jihar Adamawa mai lamba 6 na shekarar 2014, tare da sake kafawa bisa sabon tsarin doka na shekarar 2025.
Amincewar da aka yi wa kudirin dokar ya biyo bayan gabatar da shi a karon karatu na uku a gaban majalisa, wanda Shugaban Masu Rinjaye, Hon. Mrs. Kate Raymond Mamuno ta yi yayin zaman majalisar na ranar Laraba.
A cewar bincike da nazarin kwamitin korafe-korafe na jama’a, ayyukan gwamnati da harkokin zaɓe, idan aka rattaba hannu kan dokar, za ta inganta harkokin aikin hajji, da kyautata ladabtarwa, horo da sake horar da ma’aikatan hukumar.
Kwamitin ya kuma lura cewa, bisa ga ƙa’idojin Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), Jihar Adamawa za ta shiga sahun jihohin da suka cika ka’idojin kafa cikakkiyar Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jiha.
Bayan nazarin mahimmancin kudirin dokar, Shugaban Masu Rinjaye ya gabatar da bukatar karanta dokar a karo na uku, inda Mataimakin Kakakin Majalisa, Hon. Mohammed Buba Jijjiwa ya goyi bayan hakan.
Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Bathiya Wesley, wanda ya jagoranci zaman, ya miƙa bukatar amincewa ga ‘yan majalisa, kuma sun amince da ita.
Daga nan sai ya umarci Magatakardar Majalisar da ya shirya ingantaccen kwafin kudirin dokar tare da mikawa bangaren zartaswa don ci gaba da aiki akai.