Daga Nafisa Usman
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa na Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da ficewarsa daga Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), yana mai cewa akwai sabanin ra’ayi da sabon salo da jam’iyyar ta dauka.
A cikin wata wasika mai kwanan wata 14 ga Yuli, 2025, da ya aike zuwa ga Shugaban jam’iyyar PDP na Gundumar Jada 1 a Karamar Hukumar Jada ta Jihar Adamawa, Atiku ya bayyana godiyarsa matuƙa bisa damar da jam’iyyar ta ba shi.
Atiku ya bayyana cewa wannan hukuncin nasa ya matuƙar tada masa hankali, yana mai cewa PDP ta kauce daga ginshiƙan da aka gina ta a kai. “Na ga ya zama dole in ɗauki wannan mataki sakamakon hanyar da jam’iyyar ke bi yanzu, wacce bana ganin ta dace da ainihin tushen da muka gina jam’iyyar a kai,” in ji shi.
Ya kuma yi fatan alheri ga shugabannin jam’iyyar da sauran ‘ya’yanta, tare da nuna gamsuwa da haɗin gwiwa da suka yi a baya. Ya rattaba hannu a wasikar tare da amfani da sarautar gargajiyarsa ta Wazirin Adamawa. Wasikar ta isa hannun shugabannin jam’iyyar a ranar da aka aike da ita.