DOKAR MAJALISA: Ana Shirin Ɗaukaka Kwalejin Ilimi ta Hong zuwa Jami’ar Ilimi ta Adamawa

Kokarin Shugaban Majalisar Dokoki ta Jiha ta Adamawa na Majalisa ta 8, Rt. Hon. Bathiya Wesley, na ɗaukaka Kwalejin Ilimi ta Hong zuwa matsayin Jami’ar Ilimi ta Adamawa, ya samu ci gaba a ranar Juma’a yayin da kudurin dokar ya tsallake karatu na biyu a gaban majalisar.

Kudurin dokar mai taken: “Kuduri don soke dokar kafa Kwalejin Ilimi ta Hong na shekarar 2015 (Lamba 5) da kuma ƙirƙirar sabuwar doka domin kafa Jami’ar Ilimi ta Jiha ta Adamawa da za ta maye gurbin Kwalejin Ilimi ta Hong” ya samu karatu na biyu bayan gabatar da shi a gaban majalisa ta bakin Mataimakin Shugaban Masu Rinjin Gwamnati, Hon. Ahmed Jingi Belel.

Kudurin dokar wanda Rt. Hon. Bathiya ke ɗauke da shi a matsayin wakilin gundumar Hong, na da nufin bai wa ‘yan jihar damar shiga manyan makarantu, bayar da horo da digiri da difloma a fannin ilimi, karfafa bincike a fannin koyarwa da ilmantarwa, da kuma zama cibiyar nazari da ci gaba a fannin ilimi.

A cikin muhimman manufofin kudurin har da bayar da koyarwa a fannoni kamar fasaha, zamantakewa, kimiyya, ilimin dan Adam da na aiki, tare da shirya tarurruka, bita da kwasa-kwasai masu nasaba da ci gaban ilimi.

Bayan nazari kan muhimmancin kudurin, Shugaban Majalisa Rt. Hon. Bathiya Wesley, wanda ya jagoranci zaman, ya miƙa kudurin don kada kuri’ar amincewa, inda ‘yan majalisar suka amince da shi baki ɗaya.

Daga nan ne ya miƙa kudurin zuwa Kwamitin Majalisa kan Ilimi da Ci gaban ɗan Adam domin yin karin bincike da kawo rahoto a gaba.