Daraktan Janar na Hukumar Rage Talauci da Ƙirƙirar Arziki (PAWECA), Dr. Michael Zira, ya bayyana cewa hukumar na shirin fara rabon kudaden Fintiri Business Wallet ga masu neman amfana da shirin a wannan watan Yuli, bisa umarnin Gwamna.
Dr. Zira ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a ofishinsa yayin da ya karɓi tawagar kungiyar ƙwadago ta Trade Union Congress (TUC), reshen Jihar Adamawa, a Yola.
Ya nuna farin ciki da ziyarar da kungiyar ta kawo, tare da yin alkawarin ci gaba da haɗin gwiwa da kuma goyon baya da za su kawo ci gaba, yana mai ƙarfafa su da su ci gaba da tuntubarsa duk lokacin da buƙata ta taso.
Shugaban PAWECA ya bayyana ƙudurinsu da jajircewa wajen aiwatar da aikin hukumar, musamman a ɓangaren tallafa wa matasa, mata da kuma gungun masu buƙata, kamar yadda Gwamna ya tsara.
Ya ce Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ta hannun PAWECA, ya taka rawar gani wajen rage matsanancin talauci a jihar Adamawa daga kashi 74% zuwa kashi 60%, kamar yadda kididdiga ta baya-bayan nan ta nuna.