Jagororin Gwamna 11 a Yola ta Arewa Sun Rantsar da Sabbin Jiga-jigai Karkashin Kungiyar Babson na Kowa

An gudanar da gagarumin taro na rantsar da jagorori 11 na Gwamna a karamar hukumar Yola ta Arewa, karkashin tutar kungiyar matasa ta Babson na Kowa, a dakin taro na Fadfatis da ke saman NEPA, Jimeta.

Taron ya samu halartar fitattun ‘yan siyasa, sarakunan gargajiya, dattawa, da matasa maza da mata, tare da jagorancin matashin ɗan siyasa, Turakim Shinko.

A cewar Turakim Shinko, babban manufar wannan taro ita ce karrama wani matashi jajirtacce, Aliyu Jamila Babson na Kowa, wanda ya shahara wajen taimakon al’umma ba tare da nuna bambanci ba. Ya bayyana cewa Babson matashi ne mai hangen nesa, wanda ya ba da gudummawa a fannoni da dama kamar na marayu, mata marasa mijai, matasa, ilimi, lafiya da kuma kananan sana’o’i.

Turakim Shinko ya jinjina wa irin rawar da Babson ke takawa, yana mai cewa halayensa na kirki da son alheri ne suka sa suka bukace shi da ya fito karara cikin harkokin siyasa domin ci gaba da mara wa al’umma baya.

Ya kara da cewa al’ummar Yola ta Arewa za su ba Aliyu Jamila Babson cikakken goyon baya idan ya amsa kiran da ake masa, domin sun gamsu da cancantarsa da kishin kasa.

Turakim Shinko, wanda ke cikin wadanda ke bai wa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri shawara a fannin siyasa, ya bayyana farin cikinsa da mulkin Gwamnan, yana mai cewa: “Gwamna Talakawa ne, Gwamnan Fresh Air – mu kuma Adamawa muke so ta ci gaba da zaman lafiya.”

A nasa bangaren, Alhaji Hussein Gambo Nakura ya kira ga Babson da ya amsa kiran jama’a domin ci gaban jihar.

A karshe, Turakim Shinko ya bai wa wasu da suka taka rawa wajen tallafa wa tafiyar Babson lambar yabo ta musamman, ciki har da Abdurrazak Hamidu Alkali da shugabar mata Malama Kausar Jinki, bisa gudummawar da suke bayarwa.

Taron ya kayatar da mahalarta da shagulgulan raye-rayen gargajiya, sannan an rufe shi da addu’o’in fatan Allah ya maida kowa gida lafiya kamar yadda suka zo lafiya.

Rahoto daga Hadiza Aliyu Mahmud