Salihijo Ya Kaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Y2G, Ya Umarci Mambobi Su Tabbatar da Nasarar APC

Daga Abubakar Muhammad Adamu

Ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai wakiltar ƙananan hukumomin Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da Girei (Y2G), Injiniya Ahmad Salihijo Ahmad, ya kaddamar da Daraktocin Yaƙin Neman Zaɓensa da kuma Masu Kula da Yaƙin Neman Zaɓe na Ƙananan Hukumomi, domin fara shirye-shiryen yakin neman zaɓen jam’iyyar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

An gudanar da bikin kaddamarwar a ofishin yaƙin neman zaɓensa da ke Yola, inda shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki, magoya baya, mata da matasa suka hallara domin shaida ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen.

Yayin da yake kaddamar da kwamitin, Injiniya Ahmad Salihijo Ahmad ya bukaci mambobin su kasance masu biyayya, jajircewa da kuma aiki bisa manufofi da akidun jam’iyyar APC, tare da haɗa kai wajen wayar da kan al’umma da kuma neman goyon bayan jama’a a faɗin mazabar.

Ya kuma umarci kwamitin da ya yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a dukkan matakan zaɓen shekarar 2027, ciki har da zaɓen Shugaban Ƙasa domin mara wa Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu baya, zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa na Ahmed Galadima Aminu, zaɓen Sanata na Kwamared Mustapha Salihu, da kuma zaɓen kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya ta mazabar Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da Girei.

Ɗan takarar ya bayyana kwarin gwiwarsa kan ƙwarewa da gogewar mambobin kwamitin, yana mai cewa sun ƙunshi mutane masu nagarta da za su jagoranci yaƙin neman zaɓe cikin hikima tare da tabbatar da nasarar jam’iyyar. Haka kuma ya yi alƙawarin wakilci nagari, adalci da ci gaban al’umma idan aka ba shi dama ya wakilci mazabar.

Tun da farko, Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen ya bayyana cewa ƙaddamar da kwamitin alama ce ta fara shirye-shiryen da za su kai saƙon jam’iyyar zuwa ga al’ummar mazabar. Ya kuma bukaci mambobin da su ɗauki wannan nauyi a matsayin hidima ga jam’iyya da al’umma, tare da gudanar da ayyukansu cikin haɗin kai, jajircewa da gaskiya.

Da yake jawabi a madadin mambobin da aka kaddamar, Daraktan Tsare-tsare da Dabaru, Adamu Baba Mustafa, ya gode wa Injiniya Ahmad Salihijo Ahmad bisa amincewar da ya nuna a gare su. Ya tabbatar masa da cewa kwamitin zai yi aiki ba dare ba rana wajen wayar da kan jama’a da tattara goyon baya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027.

An kammala taron ne inda mambobin kwamitin suka sake jaddada aniyarsu ta fara aiki nan take, yayin da magoya bayan jam’iyyar suka bayyana ƙaddamarwar a matsayin farkon wani sabon babi na tafiyar siyasar APC a mazabar Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da Girei.