Wannan Nasara Ta Kowa Ce— Salihijo Ya Gode wa Magoya Bayansa, Ya Kammala Ziyarar Godiya a Y2G

Daga Abubakar Muhammad Adamu

“Wannan nasara ta kowane shugaba na jam’iyya ce, ta wakilai, masu ruwa da tsaki da dukkan magoya bayan da suka yi imani da hangen nesanmu. Tare za mu gina Y2G mai ƙarfi da ci gaba.” Wannan shi ne saƙon ɗan takarar kujerar Majalisar Wakilai ta Tarayya na jam’iyyar APC mai wakiltar mazabar Yola North, Yola South da Girei (Y2G), Engr. Ahmad Salihijo Ahmad, wanda aka fi sani da Kainuwa Adamawa, yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a lokacin ziyarar godiya da ya kai sassan mazabar.

Engr. Ahmad Salihijo Ahmad ya bayyana matuƙar godiyarsa bisa gagarumin goyon bayan da ya samu, wanda ya ba shi damar zama ɗan takarar jam’iyyar APC. Haka kuma, ya gode wa sauran waɗanda suka nemi takarar tare da shi saboda haɗa kai da nuna cikakken goyon baya bayan kammala zaɓen fidda gwani, tare da tabbatar da aniyarsu ta yin aiki domin tabbatar da nasarar APC a zaɓen shekarar 2027.

Ya kuma sake jaddada kudirinsa na samar da wakilci mai adalci, mai sauraron jama’a da kuma mai mayar da hankali kan buƙatun al’umma domin inganta ci gaba mai ɗorewa a mazabar Yola North, Yola South da Girei.

Ziyarar godiyar ta gudana ne a ƙananan hukumomin Yola North, Yola South da Girei, inda aka shirya ta domin gode wa shugabannin jam’iyya, wakilai, masu ruwa da tsaki da magoya baya bisa amincewar da suka nuna masa a lokacin zaɓen fidda gwani, wanda ya kai ga fitowarsa a matsayin ɗan takarar APC domin zaɓen shekarar 2027.

A duk wuraren da tawagar ta ziyarta, dubban magoya baya, ‘yan jam’iyya da shugabannin al’umma sun fito domin tarbar tawagar, tare da sake tabbatar da biyayyarsu ga jam’iyyar APC da kuma alƙawarinsu na yin aiki tukuru domin samun nasarar jam’iyyar a babban zaɓen da ke tafe.

Da yake jawabi a yayin ziyarar, Darakta Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Engr. Ahmad Salihijo Ahmad, Hon. Adamu Ibrahim Wakili, ya bayyana cewa an shirya ziyarar ne domin nuna godiya ga ‘yan jam’iyya bisa amincewar da suka yi wa Engr. Ahmad Salihijo Ahmad ta hanyar zaɓensa a matsayin ɗan takarar APC na mazabar Y2G. Ya kuma roƙi al’umma da su ci gaba da ba shi goyon baya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen shekarar 2027.

Shi ma da yake nasa jawabin a Yola North, tsohon ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar mazabar Yola North, Yola South da Girei, Hon. Abba Girei, ya bayyana Engr. Ahmad Salihijo Ahmad a matsayin shugaba nagari, mai aminci, jajirtacce kuma mai cikakken ƙwarewar da za ta ba shi damar samar da ingantaccen wakilci idan aka zaɓe shi. Ya tabbatar wa al’umma cewa ɗan takarar APC ba zai ba su kunya ba, tare da jaddada cewa haɗin kai shi ne ginshiƙin samun nasarar jam’iyyar APC a babban zaɓen da ke gabatowa.